UN-Libya
Majalisar Dunkin Duniya zata taimakawa Libya
Sakataren Janar na Majalisar Dunkin Duniya, Ban Ki-moon, yace Majalisar zata taimakawa Libya, wajen komawa tafarkin demokradiya, baya ya kai ziyara kasar.Ban yace abinda Libya ke bukata yanzu shi ne, ‘Yancin kawo karshen fargaba da tsoro da rashin gaskiya da kuma kariya daga mulkin kama karya, inda yace Majalisar zata ci gaba da taimaka sabuwar gwamnatin kasar wajen tabbatar da haka, da kuma kare Hakkin Dan Adam.
Wallafawa ranar: