Isa ga babban shafi
Liberiya

Sirleaf ta lashe zaben shugaban kasa a Liberiya

Hukumar Zabe a kasar Liberiya, ta bayyana Ellen Johnson Sirleaf a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasa, bayan samun sama da kashi 90 na kuri’un da aka kada.A lokacin da take Jawabi Bayan bayyana sakamakon zaben  Sirleaf ta yi alkawarin hada kai da 'Yan adawa da suka kauracewa zaben don gina kasa.Norris Tweah Kakakin gwamnatin Sirleaf yace shugabar ta sha alwashin mika wasu manyan mukaman gwamnati ga ‘yan adawa domin neman sasanta zaman lafiya a cikin kasar.Sirleaf ta shiga zaben ne ba tare da hamayya ba bayan da Tubman babban mai adawa da ya yi kira ga magoya bayansa da su kauracewa zaben duk da sunansa ya fito a takardar kada kuri’a.Bayan barkewar zanga-zanga ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsuhuwa domin tarwatsa magoya bayan Jam’iyyar adawa ta CDC da suka fito saman tituna suna gudanar da zanga-zanga inda mutane biyu suka mutu.Wannan zaben shi ne karo na farko da gwamnatin farar hula ta gudanar a cikin kasar tun bayan shekaru 14 bayan kawo karshen yaki a shekarar 2003. 

Shugabar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf, a lokacin da take yakin neman zabenta.
Shugabar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf, a lokacin da take yakin neman zabenta. REUTERS/Luc Gnago
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.