Isa ga babban shafi
libya-ICC

An cafke Sanusi amma za’a gurfanar da Seif a Libya

Sabbin Mahukuntan kasar Libya sun sanar da cafke Abdallah Sanusi babban na hannun damar Marigayi Muammar Gaddafi, amma gwamnatin tace a cikin kasar ne za’a gurfanar da Saif al Islam da aka kama tun da farko sabanin mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.Sabuwar gwamnatin tana kokarin watsi da matsin lambar kasashen yammaci wadanda ke neman mika Seif ga kotun duniya ta ICC a Hague inda sabbin mahunkuntan Libya suka ce a cikin kasarsa ne za’a gurfanar da shi.Sai dai manyan kasashen duniya suna ganin da wuya a kwatanta gaskiya ga shari’ar Sief saboda bindige mahaifinshi Gaddafi bayan kama shi.Tuni dai kotun duniya ta ICC ta bada sammacin kamo Seif al Islam bisa zarginsa da keta hakkin bil’adama da aikata laifukan yaki lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin mahaifinshi Kanal Gaddafi.A hirar shi da kamfanin Dillacin labaran Faransa AFP, Ministan Shari’ar kasar Libya yace a cikin kasar ne za’a gurfanar da Sief domin shari’ar gida ita ce hukunci, Shari’a a waje kuma wani abu ne daban. Kuma yace zasu kamanta gaskiya ga shari’ar.Amma kuma mai Magana da yawun kotun ICC Fadi Al-Abdallah ya nemi mahukuntan Libya su bada hadin kai domin mika Seif al Islam ga kotun bisa yarjejeniyar Majalisar Dunkin Duniya kan Libya.Yanzu haka kasashen Duniya sun bukaci Libya mutunta dokokin Duniya kan wadanda ake tuhuma da keta hakki tare da kiran sabbin mahukuntar kasar su bi umurnin kotun ICC.  

Seif al-Islam,  da Abdallah al-Sanusi babban na hannun damar Kanal Gaddafi
Seif al-Islam, da Abdallah al-Sanusi babban na hannun damar Kanal Gaddafi REUTERS/Paul Hackett/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.