Mawallafin Jaridar Gurdian a Najeriya ya mutu yana da shekaru 62
Allah Ya yi wa Alex Ibru rasuwa shugaba kuma mawallafin Jaridar Guardian a Najeriya, yana da shekaru 62 na haihuwa bayan ya dade yana jinyar rashin lafiya.
Wallafawa ranar:
Sani Mohammed Zoro
An haifi Ibru ne a shekarar 1945 a yankin Agbhara-Otor dake Jahar Delta kudancin Najeriya.
A shekarar 1983 ne ya samar da jaridar Guardian daya daga cikin jaridun harshen Turanci da suka yi fice a Najeriya musamman yankin kudancin kasar. Mista Ibru ya taba rike mukamin Ministan cikin gida tsakanin shekarar 1993 zuwa 1995 zamanin mulkin Marigayi Sani Abacha.
Tsohon shugaban kungiyar 'Yan Jaridu a Najeriya Sani Mohammed Zoro yace jaridar Ibru ta Guardian ta inganta aikin jarida a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu