Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya nada Lamorde matsayin sabon Shugaban EFCC

Bayan sallamar Farida Waziri Fadar Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta sanar da nada Ibrahim Lamorde matsayin sabon shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

Farida Waziri tsohuwar Shugabar Hukumar EFCC  Najeriya
Farida Waziri tsohuwar Shugabar Hukumar EFCC Najeriya @Next
Talla

Farida Waziri ta Fuskanci kalubalen gudanar da aikin hukumar yadda ya dace tun bayan da ta karbi aikin shugabancin hukumar a shekarar 2008.

An maye gurbinta ne da Ibrahim Lamorde wanda ya taba shugabancin hukumar na rikon kwarya.

Lamorde ya taba zama mataimakin Nuhu Ribadu tun a shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 da aka sallami Ribadu.

A watan Agusta kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta fitar da wani rehoton da ke nuna gazawar Farida Waziri wajen yaki da cin hanci a Najeriya. Kuma a rehoton ne ta bukaci shugaba Jonathan gudanar da bincike kan shugabancinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.