Isa ga babban shafi
Morocco

An fara kada kuri’a a zaben ‘Yan Majalisu a Morocco

A yau Juma’a ne al’ummar kasar Morocco ke kada kuri’ar zaben ‘Yan Majalisu bayan amincewa da sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar a watan Yuli inda Majalisar da Fira Minista zasu taka rawa a siyasar kasar.

Taswirar kasar Morocco
Taswirar kasar Morocco CIA World Factbook
Talla

An haramta gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a a cikin kasar amma masu sa ido a zaben sun yi hasashen Jam’iyyar adawa ce ta JDP zata taka muhimmiyar rawa a zaben kamar Jam’iyyar Ennahda ta musulunci a kasar Tunisia.

Jam’iyyun Siyasa 31 ne suka shiga zaben domin neman kujerun karamar Majalisa mai Wakilai 395. Cikin Jam’iyyun akwai 70 da suka shiga zaben shekarar 2007.

Wannan zaben shi ne na farko bayan samar da sabon kundin tsarin mulki da aka tabbatar a zaben jin ra’ayin Jama’a da aka gudanar a watan Yuli. Domin kaucewa zanga-zangar da ta yi awon gaba da wasu shugabannin kasashen Larabawa.

A Sabon kundin tsarin kasar, Majalisar kasar ce zata taka muhimmiyar rawa tare da karfafa mukamin Fira Minista wanda Sarki zai nada daga Majalisar da ta lashe yawan kujeru a Majalisar.

Da karfe 8:00 na safe ne aka bude runfunar zabe, ana sa ran karfe 7:00 na yamma a rufe zaben inda kuma za’a jira sakamakon zaben cikin sa’o’I 12.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.