Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Cote d’Ivoire ta mika Gbagbo zuwa Hague

A yau laraba ne gwamnatin Cote d’Ivoire ta mika tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo zuwa Hague kotun hukunta manyan laifuka, wanda shi ne shugaba na farko da zai gurfana gaban kotun tun bayan kafa ta a shekarar 2002.

Jirgin saman da ya dauko  Laurent Gbagbo, zuwa birnin  Rotterdam na kasar Holland.
Jirgin saman da ya dauko Laurent Gbagbo, zuwa birnin Rotterdam na kasar Holland. REUTERS/Robin van Lonkhuijsen
Talla

Kotun da ke farautar Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir kan kisan kiyashin yankin Darfur da binciken rikicin kasar Kenya da Libya da Jamhuriyyar Africa ta tsakiya, har yanzu ba tace komi ba kan sammacin na Gbagbo.

Sai dai wannan wata nasara ce ga shugaban kotun mai gabatar da kara Luis Moreno-Ocampo wanda ya kwashe shekaru yana farautar wadanda kotun ke zargi.

Sammacin na Gbagbo na zuwa ne bayan da kotun ta kaddamar da binciken rikicin siyasar kasar daya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamban bara, bayan da Laurent Gbagbo ya ki amincewa ya mika mulki ga Alassane Ouattara wanda duniya ta amince shi ya lashe zaben.

An kawo karshen rikicin ne bayan da dakarun Alassane Ouattara suka cafke Gbagbo a ranar 11 ga watan Afrilu.

Rikicin Siyasar kasar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3,000, da raunata wasu da dama tare da yi wa mata fyade da keta hakkin Bil’adama.

Sai dai babu wani na hannun damar Ouattara da kotun ta zarga ko ta cafke da ake zargin ya keta hakkin wasu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.