Isa ga babban shafi
IMF-Afrika

Lagarde ta fara ziyara Najeriya a Ziyararta kasashen Afrika

Shugabar Hukumar Bada lamuni ta Duniya, Christine Lagarde, ta fara ziyara aiki a Najeriya, inda ake saran zata gana da shugaba Goodluck Jonathan, da Minsitan kudin kasar, Ngozi Okonjo Iweala, kafin gobe talata ta halarci wani taro kan zuba jari a Afrika, wanda za’ayi a birnin Lagos.

Shugaban hukumar Bada lamuni ta Duniya,Christine Lagarde kusa da Tambarin hukumar.
Shugaban hukumar Bada lamuni ta Duniya,Christine Lagarde kusa da Tambarin hukumar. REUTERS
Talla

Ana saran bayan ganawa da shugaban Najeriya za ta tashi zuwa Jamhuriyar Nijar, domin ganawa da shugaba Muhammadou Yussufu.

Najeriya ita ce kasar da ta fi kowace kasa yawan mutane a Nahiyar Afrika, kasar da kuma ta fi ko wace kasa a Afrika fitar da Man Fetur, amma kuma Cin hanci da Rashawa ya yi wa kasar katutu.

Ana sa ran ziyarar Lagerde zata mayar da hankali wajen tattauna batutuwan da suka shafi samar da aikin yi ga matasan Nahiyar Afrika, domin mafi yawancin kasashen Afrika sun dogara ne da kasashen Turai da ke saka jari a Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.