Isa ga babban shafi
Nigeria

Shugaban Nigeria Jonathan ya yi tir da hallaka mutane 40 cikin hare hare

Shugaban kasar Tarayyar Nigeria Goodluck Jonathan ya yi tir da hare hare da aka kai kan majami’u yayin cikin Kirsemeti na jiya Lahadi da kuma wani harin kan jami’an tsaro, da suka yi sanadiyar hallaka akalla mutane 40.

REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Hari mafi muni an kai kan wata majami’a dake Madala kusa da Abuja, wanda ya hallaka mutane 27, yayin da ‘yan sanda suka bankado wadanda suka yi yunkurin jefa bam a wata jami’ar dake garin Jos. Hari kan hukumar tsaron ciki ya hallaka dan kunar bakin wake da jami’an tsaro uku a garin Damaturu.

Manyan kasashen duniya duk sun yi tir da harin na jiya da aka kai wasu sassan Tarayyar ta Nigeria.

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Benedict na 16, ya yi addu’oin neman samun zaman lafiya wa kasashe.

Paparoma dan shekaru 84 da haihuwa, ya nemi kawo karshen jubar da jinni a kasar Siriya, tare da neman juyin juya halin kasashen Larabawa ya zama alheri.

Addu’oin sun zo bayan hare hare da aka kai Tarayyar Nigeria kasa mafi yawan mutane cikin Nahiyar Afrika, wadda kuma sabani da rashin yarda ke kara kunno kai tsakanin addinai. Hare haren na jiya da duniya ta yi tir da su, sun yi sanadiyar hallaka mutane akalla 40.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.