AU ta tsawaita shugabancin Jean Ping har zuwa watan Yuni
Kungiyar kasashen Afrika ta tsawaita wa’adin babban Jami’inta Jean Ping har zuwa wani zaman Taron da za’a gudanar a Malawi a watan Yuni bayan gudanar da zaben da ya fuskanci hamayya daga Nkosazana Dlamini-Zuma ‘Yar kasar Afrika ta kudu.
Wallafawa ranar:
Shugabar kasar Benin kuma shugaban kungiyar Thomas Boni Yayi, yace sun yanke hukuncin tsawaita wa’adin shugabancin Mista Ping ne har zuwa wani zaman taron.
Zaben shugabannin kungiyar ne ya mamaye zaman taron a kasar Habasha, inda kuma shugabannin kasashen suka hadu domin tattauna hanyoyin magance rikice rikice a Nahiyar tare da inganta huldar cinikayya.
Shugaban kasar Zambia Michael Sata, ya shaidawa manema labari cewa an gudanar da zabe tsakanin Jean Ping da Nkosazana Dlamini-Zuma amma babu wanda ya samu rinjayen kuri’u.
Sarki Farenti Elleman
Wannan ne taro na farko da shugabannin Afrika suka gudanar tun bayan mutuwar shugaban Libya Kanal Gaddafi wanda ke tallafawa kungiyar wanda kuma ke dasawa da kasashe masu amfani da harshen Faransanci.
A ranar Lahadi shugabannin kungiyar suka zabi shugaban kasar Jamhuriyyar Benin a matsayin sabon shugaban kungiyarsu.
Sai dai taron na kungiyar na zuwa a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tashe tashen hankula a kasashen kudancin Sudan da Najeriya da Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu