Majalisar Rikon Libya ta sake zaben shugabanta
Majalisar Rikon kwaryar kasar Libya, ta sake zaben Mustafa Abdel Jalil a matsayin shugaban ta, kana kuma an sama masa maitaka guda biyu, da suka hada da Mustafa al Harun, da Salim Qanan.
Wallafawa ranar:
Wani jami’in Majalisar, Mustafa Landey, ya ce shugabanin zasu rike mukamin nasu, har sai an gudanar da zabe a watan Yuni mai zuwa. An kafa majalisar rikon yayin juyin juya halin kasar da ya yi sanadiyar kawar da gwamnatin Marigayi Shugaba Muammar Gaddafi cikin shekarar data gabata ta 2011.
Yanzu kasar ta Libya tana fuskantar kalubalen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalia tare da kwace makamai daga hanun tsaffin baraden da suka yi yakin kawar da gwamnatin Gaddafi ta shekaru 42.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu