Isa ga babban shafi
Mali

Kalaman Shugaba Toumani Toure na Mali a hirar shi da RFI

Hambararren shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Toure wanda har yanzu ba a san mabuyarsa ba tun bayan kifar da gwamnatinsa a ranar 22 ga watan Mayu, a jiya Laraba ya shaidawa Rediyo Faransa cewa yana cikin birnin Bamako kuma cikin koshin Lafiya amma ba hannun Soji ba.

Hambararren shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Touré.
Hambararren shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Touré. REUTERS/Toussaint Kluiters/United Photos/Files
Talla

A cewar Mista Toure, Babu shakka Sojoji sun nuna rishin amincewarsu da mulkin shi, amma yace kada su manta al’ummar Mali ce suka zabe shi don haka wannan gurgunta mulkin Demokradiyya ne.

Shugaban ya kara da cewa “lalle kasarmu tana fuskantar matsaloli, amma a matsayin dan kasa kuma tsohon Sojin kasar ba abun da ke da mahimmanci kamar ci gaban kasarmu Mali”.

Mista Toumani yace yana cikin kasar Mali kuma ba zai je ko ina ba,

“Babu fatan da zan yi, sai fatan cim ma bukatar kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS domin bada shawara ta gari. Idan baku manta ba wata daya ne kacal ya rage wa’adin mulki na ya kawo karshe”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.