Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Al Bashir ya yi gargadin kifar da Gwamnatin Sudan ta Kudu

Shugaban kasar sudan Umar Hassan Al Bashir ya yi gargadin kifar da gwamnatin Sudan Ta Kudu bayan karbe ikon yankunan da ke da albarkatun Mai, tare da zargin kasashen duniya wajen hura wutar ballewar yaki tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir a lokacin da yake jawabin kaddamar da yaki a Sudan ta Kudu gaban daruruwan dakarun Sudan da magoya bayan shi.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir a lokacin da yake jawabin kaddamar da yaki a Sudan ta Kudu gaban daruruwan dakarun Sudan da magoya bayan shi. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Al Bashir yana Magana ne a gaban dakarun Sudan wadanda za’a tura yaki domin karbe ikon yankin Heglig.

“zamu fara yaki a Heglig amma zamu kammala a Juba”, a cewar Al Bashir.

Majalisar Dinkin Duniya da kasar Amurka da Tarayyar Turai dukkaninsu sun yi Allah Waddai da Sudan ta Kudu bayan karbe Ikon yankin Heglig tare da la’antar hare haren da Sudan ta kaddamar a yankunan Kudancin Sudan.

Rikicin kasashen biyu yanzu ya kazanta,kusan shi ne mafi muni tun bayan samun ‘yancin Kudanci a watan Yulin bara bayan yakin basasa a shekarar 1983-2005 da ya yi sanadiyar salwantar rayuka sama da Mliyan Biyu.

Sai dai bayan jin kalaman Al Bashir, Sudan ta Kudu ta yi kiran sasantawa kamar yadda ministan yada Labaran kasar Barnaba Marial Benjamin, ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.