Isa ga babban shafi
Masar

An shiga rana ta biyu a Zaben Masar

A kasar Masar, an bude runfunan zabe a rana ta biyu a zaben shugaban kasa na farko mai dimbin tarihi domin zaben wanda zai gaji Hosni Mubarak wanda zanga-zanga ta yi awon gaba da shi a bara. Wannan Zaben shi ne zai kasance mizanin ci gaban kasar. 

Wasu  mata 'Yan kasar Masar suna kada kuri'arsu a runfar zabe a birnin Al kahira.
Wasu mata 'Yan kasar Masar suna kada kuri'arsu a runfar zabe a birnin Al kahira. Reuters/Ammar Awad
Talla

Miliyoyin al’ummar Masar ne suka fara kada kuri'a a rana ta biyu.

Da misalin karfe 8:00 na Safe Agogon kasar ne aka bude runfunan zabe

Ana sa ran a samu yawan masu kada kuri’a a rana ta biyu fiye da jiya Laraba da aka fara zaben bayan gwamnatin kasar ta bada hutu ga ma’aikata domin kada kuri’arsu.

A rana ta farko, an gudanar da zaben cikin lumana kodayake an samu wasu kurakurai da masu sa ido suka ce sun gani.

Wannan shi ne zaben farko a Tarihin Masar.

Ana sa ran masu kada kuri'a miliyan 50 ne za su kada kuri’ar zaben shugaban kasa tsakanin ‘Yan takara goma sha Biyu masu neman kujerar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.