Isa ga babban shafi
Masar

Brotherhood ta yi ikirarin lashe zaben shugaban kasa a Masar

Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Brotherhood a Masar tace dan takararta Muhammed Mursi ya kada Ahmed shafiq a zaben shugaban kasa, bayan lashe sama da kashi 52 na kuri’un da aka kada. Sai dai bangaren Ahmed Shafiq sun yi watsi da ikrarin Jam’iyyar.

'Yan Uwa Musulmi sun murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa da dan takarar Jam'iyyar Brotherhood Mohammed Mursi ya samu a ikirarinsu
'Yan Uwa Musulmi sun murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa da dan takarar Jam'iyyar Brotherhood Mohammed Mursi ya samu a ikirarinsu Reuters
Talla

Sai dai gwamnatin Sojin Masar ta yi shelar wata doka da zai bata damar gudanar da ayyukan Majalisar kasar da kotu ta rusa a makon jiya.

Karkashin dokar, babu wani zabe da za’a sake gudanarwa har sai an rubuta kundin tsarin mulki, yayin da a bangare daya ake kallon matakin a matsayin wani shiri na murde zaben shugaban kasa.

Idan aka tabbatar da nasarar Mursi, zai kasance shugaban Masar na Farko daga ‘Yan Uwa musulmi.

Amma Ahmed Shafiq wanda Fira Ministan Gwamnatin Mubarak ne kuma abokin hamayyar Mursi ya fito ya karyata ikirarin Brotherhood na lashe zabe.

Yanzu haka dai daruruwan magoya bayan Jam’iyyar Brotherhood ne suka fito domin murnar nasar lashe zabe a Hedikwatar Jam’iyyar.

A yakin neman zaben shi Mursi, ya sha alwashin aiki tare da al’ummar Masar Musulmi da kirista domin samun ci gaba mai dorewa da samar da zaman lafiya da kuma ci gaban Demokradiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.