Sudan da Sudan ta Kudu sun sasanta kansu game da Fetir
Kasashen Sudan da Sudan ta kudu sun cim ma yajejeniyar biyan jingar safarar Man Fetir a tsakaninsu al’amarin da ya yi yunkurin jefa kasashen cikin yaki. Ana tunanin wannan matakin zai iya kawo karshen sabanin da ke tsakanin kasashen biyu.
Wallafawa ranar:
Thabo Mbeki wanda ya shiga tsakanin sasanta kasashen biyu, yace bangarorin biyu sun sasanta sabanin da ke tsakaninsu akan Man Fetir, kwanaki biyu da kawo karshen wa’adin da Majalisar Dinkin Duniya ta basu.
Sudan ta Kudu ta amince ta biya Sudan kudi Dala ($) 9.48 duk ganga domin shigo da manta ta hanyar bututun man Sudan.
Shugabannin kasashen duniya da dama sun yaba da wannan matakin tare da neman kasashen sun sasnata sauran sabanin da ke tsakaninsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu