Isa ga babban shafi
DRC Congo-Rwanda

Kagame da Kabila za su gana don inganta tsaro a kasashensu

Shugabannin kasashen Rwanda da Jamhuriyar Democradiyyar Congo za su gudanar da wani taro a Uganda game da inganta tsaro a iyakokinsu tare da niyyar samar da Dakaru da za su fafata da ‘yan tawaye.

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame tare da Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame tare da Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila
Talla

Shugaban kasar Uganda Yoweri Musaveni zai kasance mai masaukin baki, a taron na kwanaki biyu da za’a gudanar a wani wajen taro da ke bayan garin Kampala.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da takwaransa na Congo, Joseph Kabila dukkaninsu sun bada tabbacin za su samu halartar taron.

Akwai wakilai da Majalisar Dinkin Duniya zata tura a wajen taron da ke da niyyar warware takaddamar da ke tsakanin kasar Rwanda da kasar Janhuriyar Democradiyyar Congo, wadanda ke zargin juna da tallafawa ‘yan tawaye.

A Jiya Litinin ne Ministocin waje na kasashen yankin suka gudanar da taron share fage.

Idan har aka cim ma matsaya a taron kasashen yankin za su samar da Dakarun hadin kai, sannan kuma su samar da kudaden da suka wajaba domin ayyukan Dakarun.

Kungiyar Tarayyar kasashen Africa ta nuna goyon baya tare da alkawalin shirin tallafawa tsarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.