Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kira jakadanta da ke kasar Rwanda

Kasar Faransa ta janye jakadanta daga kasar Rwanda sakamakon yadda kasar ta Rwanda ta ki amincewa da sabon jakadan Faransa data tura Rwandan.

Talla

Mai Magana da yawun Ma'aikatar waje na Faransa Vincent Floreani, ya fadi cewa Faransa ta janye jakadan nata ne domin ta nazarci inda aka sa gaba, da kuma tattaunawa da jakadan sosai.

Wasu bayanan na cewa kasar Rwanda ta ki amincewa da sabuwar jakadiyar ce saboda ta kasance na hannun daman Ministan waje na Faransa Alain Juppe.

Shidai Alain Juppe, wanda ya ke Ministan harkokin waje a lokacin kisan kiyashi a Rwanda a shekarar 1994 ya yi alkawari babu abinda zai sashi ya sha hanu da Shugaba Paul Kigame na Rwanda, sakamakon rahoton 2008 da ke zargin Faransa ha hannu cikin rikicin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.