Isa ga babban shafi

Rasha ta sanya shugaban Ukraine a kundin masu laifi da ta ke nema ruwa a jallo

Rasha ta sanya shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a cikin kundin sanayen masu aikata laifuka da ta ke nema ruwa a jallo, matakin da Ukraine ɗin ta yi watsi da shi, tana mai cewa Rasha ta ruɗe ne kawai.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. REUTERS - ALINA SMUTKO
Talla

A ranar Asabar ce sunan Zelensky ya bayyana a cikin kundin ma’aikatar cikin gidan Rasha na masu laifin da mahukuntan ƙasar ken nema ido rufe, inda ma’aikatar ta ce ana neman shugaban Ukraine ne a ƙarkashin kundin dokar hukunta masu aikata laifuka ba  tare da ta yi wani ƙarin bayani ba..

Zalika, babu wani bayani daga mahukuntan Rasha a kan dalilin da ya sa aka sanya sunan shugaban Ukraine a cikin wannan kundi.

A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce matakin Rashi na nuni da ruɗewa da masu farfagandanta suka yi a kan abin da za su ƙirƙiro don jan jan hankalin duniya.

A shekarar da ta gabata, shugaban Ukraine ya bayyana cewa yana sane da yadda aka daƙile yunƙurin yi masa kisan gilla har sau shida, kuma yana zargin Rasha ne da hakan.

Kwana guda bayan da ya aike da dakarun ƙasar Ukraine, shugaban Rasah, Vladimir Putin ya yi wani jawabi, inda ya ke neman rundunar sojin Ukraine ta yi wa Zelensky juyin mulki.

Rasha ta sanya sunayen ɗimbimm ƴan siyasa na ƙasashen waje a cikin wannan kundi naata, mai ɗauke da dubban sunaye.Russia has placed several foreign politicians and public figures on its wanted list, which has tens of thousands of entries.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.