Isa ga babban shafi

Ukraine ta ce ta daƙile shirin Rasha na yi wa shugaba Zelensky kisan gilla

Hukumar leken asirin Ukraien ta ce ta daƙile wani sshirin da Rasha ta yi na yi wa shugaba Volodymyr Zelensky kisan gilla.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. REUTERS - ALINA SMUTKO
Talla

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata nan, hukumar leƙen asirin ta ce ta bankaɗo wani gungun masu leken asiri a ƙarƙashin hukumar tsaron Rasha, wadda ke aikin kitsa yadda za a kashe shugaba Zelenskyy da wasu manyan ƴan siyasar da hafsoshin sojin Ukraine.

Sanarwa ta ƙara da cewa an kama wasu sojoji biyu masu muƙamin kanar, waɗanda ke bai wa manyan jami’an Ukraine kariya bisa zargin ƙoƙarin aiwatar da  shirin na Rasha, inda ake zargin su da cin amanar ƙasa.

A  cewar sanarwar, Rasha ta yi aikin gano waɗanda ke kusa da masu bai wa  Zelenskyy kariya, inda ta ƙara da cewa an ɗauki  kanar-kanar ɗin aiki ne gabanin mamayar da Rasha ta wa Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Ta ce an bai wa hafsoshin biyu aikin nemo wani na kusa da Zelenskyy, wanda zai yi garkuwa da shi, daga bisani kuma ya kashe shi, ammma sai suka yi rashin sa’a aka bankaɗo shirinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.