Isa ga babban shafi

Shugaban China na ziyara a Paris don ƙarfafa dangantakar kasuwanci da Faransa

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen sun buƙaci China ta tabbatar da ƙarin daidaito a kasuwancin da ke tsakanin.Wannan na zuwa ne a yayin wata ziyara da shugaba Xi Jinping ya fara a Paris, inda ake sa ran  Macron ya tinkare shi da batun yaƙin da ake a Ukraine.

Xi Jinping na China da mai masaukinsa Emmanuel Macron na Faransa.
Xi Jinping na China da mai masaukinsa Emmanuel Macron na Faransa. © Gonzalo Fuentes / Reuters
Talla

Ziyarar Xi zuwa Turai a karon farko cikin shekaru biyar kenan, a  daidai lokacin da ake samun ta’azzarar tankiya ta kasuwanci da suka haɗa da binciken da Tarayyar Turai ke yi a kan masana’antun China da ke ƙera kayayyaki kamar motoci masu amfani da lantarki a yayin da ita China ke bincike a kan akasari kayayyaki dangin barasa da ke shiga ƙasarta daga Faransa.

Macron ya ce akwai buƙatar Turai da China su warware matsalolin da ke tsakanin su, musamman ma ta kasuwanci, yana mai cewa makomar nahiyar  tasu ta ta’allaaka ne ainun a kan ingantawa tare da samar da daidaito a kan dangantakarta da China.

Ita ko Von der Leyen ta fi fitowa ƙarara, inda ta ce danganta da ke tsaninsu tana samun naƙasu ne sakamakon rashin daidaito a kasuwanci, da kuma tallafi da China ke bai wa masana’antunta.

A tsokacin da ya yi gabanin tattaunawar,  shugaba Xi ya ce China na ɗaukar dangantaka tsakaninta da Turai a matsayin ɓangare mai mahimanci na manufofinta na hulɗa da ƙasashen waje, saboda haka kamata ya yi dukkaninsu su yi abin da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.