Libya
An Zabi Mohamed al-Megaryef a matsayin shugaban Majalisar Libya
An zabi Mohamed al-Megaryef, wani mai tsananin adawa da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi, kuma dan kishin Islama, a matsayin shugaban sabuwar majalisar dokokin kasar Libya. Megaryef, yana cikin wadanda suka jagoranci kungiyar ceto al’ummar Libya, ya samu kuri’u 113 a zauren majalisar inda ya kayar da Ali Zidane mai kuri’u 85.
Wallafawa ranar:
Talla
A ranar Laraba gwamnatin wucin gadin kasar libya ta mika mulkin ga majalisar, abin da ke numa an sami nasarar sauyin gwamnati cikin lumana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu