Isa ga babban shafi
Kenya

Zanga-zanga ta barke a kasar Kenya bayan kisan Malamin addini

Dubban masu zanga-zanga a kasar Kenya sun yi arangama da ‘Yan Sanda a birnin Mombasa bayan kisan wani malamin Addinin Islama da ake zargin yana da alaka da kungiyar Al Qaeda. Masu zangar zangar suna zargin ‘Yan Sanda ne suka kashe Aboud Rogo Mohammed amma ‘Yan sandan sun ce suna gudanar da bincike wadanda suka kashe Malamin.

Motoci da aka kona a Brinin Mombasa a kasar Kenya
Motoci da aka kona a Brinin Mombasa a kasar Kenya REUTERS/Joseph Okanga
Talla

Daruruwan masu zanga zangar, sun farfasa gilassan motoci, tare da kone wasu majami’u Hudu, a Mombasa, bayan kashe malamin da Amurka ta zarga yana taimaka wa kungiyoyi masu kishin Islama, da ke dauke da makamai a Somalia.

Matar Malamin Haniya tace wasu mutane ne cikin mota suka bindige Mijinta suna cikin mota bayan motarsu ta kusanto kusa da su.

Tun a watan Juli ne kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya haramtawa Malamin yawo tare da dakile asusun ajiyar shi saboda alakar shi da kungiyar Al Shabeb.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.