Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Mutum daya ya rasa ransa a harin ofisoshin ‘Yan sandar Cote d’Ivoire

Akalla mutum daya ya rasa ransa bayan wasu dauke da makamai sun abkawa wasu ofisoshin ‘Yan sandan kasar Cote d' Ivoire, a garin Abidjan, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AFP. Wani mai daukan hoton AFP ya tabbatar ya ga gawar mutumin wanda farar hula ne a gefen hanya.  

Shugaban kasar Cote d'Ivoire, Alassane Outtara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire, Alassane Outtara AFP
Talla

Amma har yanzu hukumomi basu ba da adadin mutanen da su ka mutu a harin ba, tun bayan hare hare da aka kaiwa jamai’an tsaro a watan Agusta.

Akalla wani mutum daya da ake zargin na da hanu a cikin harin na hanun jami’an tsaro, a yayin da aka saka shingaye akan tituna domin binciken motoci.

Kasar ta Cote d’Ivoire ta yi fama da rikici na taswon watanni biyar wanda daga baya aka cafke Laurent Gbagbo ana tuhumarsa da laifin kisa da tauye hakkin Bil Adama.

Akalla mutane 3,000 su ka mutu a rikicin a cewar Majalisar Dinki Duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.