Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun kashe dakarun Afrika ‘Yan Najeriya guda hudu

Wasu ‘Yan bindiga sun hallaka dakarun samar da zaman lafiyan kungiyar kasashen Afrika, dake Yankin Darfur guda hudu, yayin da wasu takwas suka samu raunuka, a kwantan baunar da aka musu. 

Dakarun Afrika
Dakarun Afrika REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Kakakin dakarun dake aiki a El Geneina, yace daukacin sojojin da aka kashe ‘Yan Najeriya ne, sakamakon bude musu wuta da akayi.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki -Moon ya bayyana bacin ransa da harin, inda ya bukaci gwamnatin Sudan ta gudanar da kwakwaran bincike akai.

Akalla dakarun samar da zaman lafiya 42 aka kashe a Darfur, daga cikin 23,500 da aka girke a shekarar 2007.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.