Libya
An zabi tsohon mai adawa da Gaddafi a matsayin Firaministan Libya
Majalisar Kasar Libya, ta zabi wani tsohon mai adawa da shugaba Kanal Muammar Ghadafi, Ali Zeidan, a matsayin sabon Firaminista, sakamakon nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar. Shugaban kasa, Mohammed Magaryef ne ya sanar da sakamakon, inda ya bukaci sabon Firaminista kafa gwamnati a cikin makwanni biyu.
Wallafawa ranar:
Talla
Ali Zeidan, tsohon Jakadan Libya ne a India, wanda ya balle ya fara adawa da shugaba Ghadafi tun a shekarar 1981.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu