Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu wata tattaunawa tsakanin gwamnati da Boko Haram, inji Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace babu wata tattaunawa da gwamnatin shi ke yi da kungiyar Boko Haram domin kawo karshen jubar da jini a Najeriya. Shugaban kuma yace yana da wahala a sasanta da kungiyar.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Reuters/Eduardo Munoz
Talla

Shugaba Jonathan dai yana fuskantar matsim Lamba ne daga ‘Yan Najeriya wadanda suke ganin ya dace Gwamnati ta shiga tattaunawa da kungiyar da ake zargin tana kai hare haren bama bamai  da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tun  a shekarar 2009.

A watan Agusta, kakakin shugaban na Najeriya Reuben Abati yace Gwamnati ta shiga tattaunawa da wasu shugabannin kungiyar a asirce.

Amma a Lokacin da Goodluck Jonathan ke amsa tambayoyi daga ‘Yan Jaridu shugaban yace babu wata tattaunawa tsakanin Gwamnatin shi da Boko Haram, yana mai cewa babu tabbacin ko kungiyar tana da jagoran da zai jagoranci tattaunawar.

Amma akwai lokutta da dama da Abubakar Shekau yana aiko da sakon Bidiyo a You tube a matsayin Shugaban kungiyar Boko Haram.

Tun fara rikicin Boko Haram an kiyasta samun mutuwar mutane 3,000 a hare haren bama bamai da ake kai wa a yankin Arewaci da kuma Jami’an tsaro da ake zargin suna cin zarafin al’umma da sunan farautar ‘Yan kungiyar Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.