Isa ga babban shafi
Sudan

An yi yunkurin juyin mulki a Sudan

Gwamnatin kasar Sudan na tsare da wasu manyan jami’an sojan kasar 13 ciki har da tsohon shugaban Hukumar tsaron kasar, saboda zargin su da kitsa kifar da Gwamnatin kasar.Ganau sunce manyan tankunan yaki sunyi ta karakaina cikin kasar yau Alhamis, kafin wayewar gari, kuma tashar Talibijin da Radio na kasar sun yi ta cewa anyi nasarar murkushe yunkurin juyin mulkin.A shekara ta 2009 Shugaba Omar al-Bashir ya tsige tsohon babban jamiin tsaron kasar Janar Salah Gosh, a matsayin Shugaban Tsaro aka kuma maye gur binsa da mataimakin sa Janar Mohammed Atta al-Moula. 

Wasu sojan kasar Sudan
Wasu sojan kasar Sudan
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.