Isa ga babban shafi
Masar

Bangaren Shari’a a Masar sun shiga yajin aiki

Alkalan Kotunan daukaka kara a kasar Masar, sun tsunduma cikin yajin aiki, don nuna rashin amincewarsu da dokar da shugaba Mohammed Morsi da ta ba shi karfin fada aji da babu wanda zai iya kalubalantar shi.

Masu Zanga-zangar Adawa da Shugaban Masar Muhammad Morsi bayan kaddamar da dokar karawa kansa karfin fada aji
Masu Zanga-zangar Adawa da Shugaban Masar Muhammad Morsi bayan kaddamar da dokar karawa kansa karfin fada aji REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Alkalan sun ce ba zasu daina yajin aiki ba, har sai shugaban ya soke dokar. A bangare daya kuma, yau ne ake saran majalisar da ke rubuta sabon kundin tsarin mulki ta kamamla aikin ta.

Tuni dai Muhammed Morsi yace dokar karfin fada aji da ya ba kansa tana nan daram bayan ya gana da Bangaren shari’a duk da zanga-zangar adawa da dokar da al’ummar Masar ke yi, zanga-zanga mafi muni tun bayan zaben shi a watan Juni.

Fadar Shugaba Morsi ta yi ikirarin cewar dokar ta wucin gadi ce, kuma ba wai an yi ta ne don a tirsasawa wani sashe ba.

Dokar da aka bayyana a makon jiya ta haifar da zanga-zanga a sassan biranen Masar Tare da durkushe hada hadar kasuwar hannayen jari a cikin kasar.

Dokar zata ba Morsi karfin fada aji da zai iya yanke hukunci ba tare da kalubalantar shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.