Isa ga babban shafi
Masar

Morsi ya nemi sasantawa bayan kara ma kansa karfin fada aji a Masar

Shugaban Kasar Masar, Mohammed Morsi, ya bukaci ganawa da manyan alkalan kasar, don kashe wutar da ta taso, sakamakon dokar kara wa kansa karfin fada aji, al’amarin da ya janyo suka daga sassa dabam dabam, da har ya sa Alkalan kasar shiga yajin aiki.

Masu Zanga-zangar Adawa da Shugaban Masar Muhammad Morsi bayan kaddamar da dokar karawa kansa karfin fada aji
Masu Zanga-zangar Adawa da Shugaban Masar Muhammad Morsi bayan kaddamar da dokar karawa kansa karfin fada aji REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Fadar Shugaba Morsi ta yi ikirarin cewar dokar ta wucin gadi ce, kuma ba wai an yi ta ne don a tirsasawa wani sashe ba.

Dokar da aka bayyana a ranar Alhamis ta haifar da zanga-zanga a sassan biranen Masar. Tare da durkushe hada hadar kasuwar hannayen jari a cikin kasar.

Dokar zata ba Morsi karfin fada aji da zai iya yanke hukunci ba tare da kalubalantar shi ba.

Sanadiyar haka ne kuma aka samu barkewar zanga-zanga tsakanin magoya bayan Jam’iyyar Morsi ta Brotherhood da kuma masu adawa da shugaban.

Rahotanni sun ce an samu mutuwar mutum guda tare da raunata wasu mutane 10.

Ana sa ran Shugaba Morsi zai gana da Alkalin alkalan kasar domin sasantawa don kawo karshen rikicin.

Masu zanga-zanga dai sun kai wa ofishin Jam’iyyar Brotherhood hari da sauran Jam’iyyun da ke kawance da Jam’iyyar Shugaban.

Tuni dai ‘Yan adawa irinsu Mohamed ElBaradei da tsohon dan takar shugaban kasa Hamdeen Sabbahi da Amr Mussa da Abdelmoneim Abul Futuh suka ce zasu kauracewa duk wani yunkurin tattaunawa da Morsi idan har bai janye dokar ba.

Rikicin na Masar na zuwa ne bayan Shugaba Morsi ya yi kokarin shiga tsakanin sasanta rikicin Isra'ila da Faledinawa bayan kwashe mako bangarorin biyu suna luguden wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.