Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan za ta karbi bakuncin Taron kasashen D8

Shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Musulmi ta D8 za su gudanar da taro a kasar Pakistan don tattauna hanyoyin inganta huldar cinikayya tsakaninsu amma ana hasashen batun rikicin Gaza zai mamaye zaman taron. Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad da shugaban Masar Mohammed Morsi da Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan suna cikin shugabannin da za su halar ci taron na kasashe Takwas da ake kira D8.

Shugabnnin kungiyar bunkasa tattalin arziki  kasashen musulmi 8
Shugabnnin kungiyar bunkasa tattalin arziki kasashen musulmi 8 Reuters
Talla

Shugaban kasar Indonesia Susilo Bambang Yudhoyono da shugaban Najeriya goodluck Jonathan suna cikin shugabannin ake sa ran za su halarci taron. Ana tunanin Bangladesh da Malayesia za su aika da wakilansu.

Halartar Taron zai kasance karon Farko da Shugaban Masar Mohammed Morsi zai kai ziyara Pakistan a matsayin shugaban kasa. Haka kuma wannan ne karon Farko da Shugaban Najeriya zai kai Ziyara kasar Pakistan tsawon shekaru 28 da suka gabata.

Kasashen dai suna fatar inganta cinikayya ne tsakaninsu daga kudi Dala Biliyan Dari da Talatin ($130b) zuwa Dala Biliyan Dari Biyar da Bakwai ($507b) daga nan zuwa shekarar 2018.

Ana sa ran kasashen za su tattauna matsalar tabarbarewar tattalin arzikin duniya da kuma matsalar dumamar yanayi.

Akwai dai matakan tsaro da Gwamnatin kasar Pakistan ta tanada domin karbar bakuncin shugabannin saboda kaucewa barazana daga kungiyar Al Qaeda.

Ana sa ran kasashen za su yi amfani da damar taron domin tattauna rikicin Faledinawa da Isra’ila a Gaza bayan Masar da Iran da Turkiya suka yi Allah Waddai da hare haren da Isra’ila ke kai wa Falesdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.