Isa ga babban shafi
Masar

Masu zanga-zanga sun yi wa fadar shugaban Masar Da’ira

Masu Zanga-zanga a Masar da ke adawa da Shugaban Morsi sun yi arangama da ‘Yan sanda tare da kewaye fadar shugaban kasa. Rahotanni sun ce Shugaba Morsi ya fice daga fadar Itihadiya bayan ganawa da jami’ansa.

Dubban Mutane masu Zanga-zangar adawa da Shugaban Masar Mohammed Morsi sun kewaye fadar shugaban kasa
Dubban Mutane masu Zanga-zangar adawa da Shugaban Masar Mohammed Morsi sun kewaye fadar shugaban kasa REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

‘Yan Sandan dai sun yi ta harba barkonon Tsohuwa domin tarwatsa gungun masu zanga-zangar amma hakan ya ci tura.

An dai bayyana cewa yawancin masu zanga zangar magoya bayan jam’iyun da ke da ra’ayin jari huja da kuma sassaucin ra’ayi.

Wannan zanga-zangar tana cikin matakan da ‘Yan adawar Masar suka dauka, domin nuna kin yardarsu da kudirin shugaba Mohamed Morsi na karawa kansa karfin iko, da kuma kiran zaben raba gardamar da ya yi a ranar 15 ga watan Disemba domin samar da sauye sauyen a kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan Al’amarin dai ya raba kanun al’ummar kasar, inda a bangare daya magoya bayan kungiyar ‘Yan uwa musulmi suka gudanar da ta su zanga zangar nuna goyon baya ga matakin da shugaban ya dauka.

An samu rahoton fito na fito tsakanin magoya bayan Jam’iyyar Brothrhood ta Morsi da kuma masu adawa da shi a yankin Minya.

Daruruwan magoya bayan Morsi ne kuma suka fito a birnin Alexandria da yankin Sohag domin gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan shugabansu.

Wasu masu Zanga-zangar dai suna adawa ne da Mulkin Shari’a Musulunci da Morsi ke neman kafawa suna masu cewa hakan zai raba hankulan al’ummar kasar

A watan Junin shekarar 2011 ne aka rantsar da Mohammed Morsi a matsayin shugaban kasa bayan masu zanga zanga sun hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Wasu ‘Yan adawa sun ce Morsi ya dauki salon mulkin kama karya ne irin na Mubarak.

A makon jiya ne Alkalan masar suka shiga yain aiki domin adawa da matakan Morsi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.