An girke tankunan yaki a fadar shugaban Masar
Rungunar Sojin kasar Masar, ta girke tankunan yaki a fadar shugaban kasa a birnin Alkahira, bayan samun wata arangama tsakanin magoya bayan Shugaba Morsi da masu zanga-zangar adawa da shi.Rahotanni daga Alkahira sun ce an samu lafawar rikicin tsakanin masu zanga-zanga bayan samun mutuwar mutane uku wasu daruruwa kuma suka rauni.
Wallafawa ranar:
Zanga-zanga dai ta barke ne a kasar Masar domin adawa da kudirin gwamnati na yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.
Kuma gwamnatin kasar t ace za’a gudanar da zaben ra’ayin jama’a duk da adawa da shirin da wasu al’ummar kasar ke yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu