Isa ga babban shafi
Masar

‘Yan adawar Masar sun bukaci magoya bayansu su jefa kuri’ar a’a a zaben raba gardama

‘Yan adawar kasar Masar sun ce ba za su kauracewa zaben raba gardamar da za’a yi ranar Assabar mai zuwa ba, sai dai suna bukatar magoya bayansu su jefa kuri’ar kin Amincewa, domin nuna Adawa da shirin sabunta kundin tsarin mulkin kasar.

Kuriar zaben Raba gardama a kasar Masar
Kuriar zaben Raba gardama a kasar Masar REUTERS/Sharif Karim
Talla

A bangare daya kuma, kokarin rundunar sojin kasar na sasanta bangarorin da ke rikicin, wato Gwamnati shugaba Mohammed Morsi da ‘Yan adawa ya ci tura, inda aka soke shirin ganawar.

Khaled Dawud kakakin ‘Yan adawar yace sun yi kira ga magoya bayansu su jefa kuri’ar kin amincewa da kudirin.

Yanzu haka kuma Bangaren shari’a sun ce za su sa ido a zaben tare da jami’an tsaro da masu sa ido daga kasashen waje domin tabbatar da an ba Al’ummar Masar abun da suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.