Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Sandan Najeriya sun cafke wasu ‘Yan Jarida saboda sun rubuta labarin da ya sabawa Soji

‘Yan Sandan Najeriya sun Cafke wasu ‘Yan jarida biyu, bayan wallafa wani rahoton da ke zargin wasu jami’an tsaron kasar da musguna wa jama’a, a yunkurin da suke yi na kawar da ‘Yan kungiyar Jama’atu ahlus Sunna Lil Da’awati Wal Jihad da ake kira da sunan Boko Haram kamar yadda jaridun da ‘Yan Jaridar ke aiki Suka ruwaito.

Sojin Najeriya suna sintiri bayan kafa dokar hana fita a wasu biranen kudu maso yammacin Najeriya saboda rikicin Boko Haram
Sojin Najeriya suna sintiri bayan kafa dokar hana fita a wasu biranen kudu maso yammacin Najeriya saboda rikicin Boko Haram sphotos-a.xx.fbcdn.net
Talla

Babban Editan jaridar Almizan Ibrahim Musa ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa, da asubahin Jiya Litinin, jami’an tsaron, suka kai samame a gidajen Editan Jaridar, Musa Muhammad Awwal, da wakilin ta Aliyu Saleh, tare da yin awon gaba da su da iyalansu. Amma daga bisani an saki iyalansu.

Malam Ibrahim yace a lokacin da ‘Yan sandan ke samamen sun kwashe wa ‘Yan Jaridun Na’urar Kwamfutarsu da wayoyin salula a gidajensu da ke Kaduna.

An fara buga Jaridar Al Mizan ne a shekarar 1991 da harshen hausa kuma jarida ce ta mabiya akidar Shi’a da ke samun goyon baya daga gwamnatin Iran.

Tuni dai hukumom kare Hakkin Bil’adama suka zargi Jami’an tsaro da cin zarafin al’umma da sunan yaki da kungiyar Boko Haram a Arewacin Najeriya.

Amma Jami'an tsaron na Farin kaya ba su ce komi ba game da wannan Batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.