Isa ga babban shafi
Masar

An garzaya da tsohon shugaban Masar Mubarak zuwa Asibiti

Wata majiya daga masu gabatar da kara a kasar Masar, ta bayyana cewar yanzu haka an kwashi tsohon shugaban kasar, Husni Mubarak dake zaman wakafi a wani gidan yarin kasar, zuwa Assibiti.An dai bayyana cewar lafiyar Husni Mubarrak na ci gaba da tabarbarewa.Dama dai an daure tsohon shugaban ne sakamakon yadda aka same shi da laifin kisan masu zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin shi a shekarar bara.Majiyar ta ce, Mubarrak mai shekaru 84, ya fadi ne a dakin shi a gidan kaso, kuma za’a maida shi a Gidan kaso idan ya samu sauki. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.