Isa ga babban shafi
Masar

Mutane 50 sun mutu a Masar, ‘Yan adawa sun yi watsi da tayin tattaunawa da Morsi

‘Yan sandan Masar na ci gaba da arangama da Masu Zanga-zanga wadanda suka keta dokar haramta zirga-zirga a kokarin gwamnatin Morsi na kwantar da rikicin kasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 50.

'Yan sanda suna arangama da masu zanga-zanga a kasar Masar
'Yan sanda suna arangama da masu zanga-zanga a kasar Masar Reuters/
Talla

‘Yan Adawar kasar Masar, sun ki amincewa da tayin shugaba Mohammed Morsi, na shiga tattaunawa ta kasa, dominn warware matsalar da ta addabi kasar yanzu haka.

Rahotanni sun ce akalla mutane 50 suka mutu, a tashin hankalin da aka samu na baya bayan nan, sakamakon hukuncin kisan da kotu ta yanke wa mabiya kungiyar kwallon kafa a Port Said.

Shugaban ‘Yan adawar kasar, Mohammed El Baradei, yace ba za su shiga wani taro ba, dole sai shugaba Morsi ya kafa gwamnatin hadin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.