Isa ga babban shafi
Najeriya

Kamfanin Shell ya yi gargadin dakatar da aiki a Najeriya saboda Satar Mai

Kamfanin hako man fatir na shell ya yi gargadin dakatar da wasu ayyukansa a Tarayyar Najeriya sakamakon matsalar fasa bututunsa a yankin kudancin kasar. A wata sanarwa da Kamfanin ya fitar, ya bayyana daukar matakin rufe sashensa da ke samar da mai a gabar ruwan da ake kira da sunan Nembe Creek.

Bututun Mai kamfanin Shell a Jahar Bayelsa yankin Kudancin Najeriya
Bututun Mai kamfanin Shell a Jahar Bayelsa yankin Kudancin Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye /Files
Talla

Kamfanin yace wani abu ne da ya zama wajibi, sakamakon gano tsiyayar mai wadda a halin yanzu kamfanin ya ce ba zai iya fayyace dalilan faruwarta ba.

Kamfanin ya ce zai kafa kwamitin kwararru domin binciken dalilan faruwar hakan, kuma tawagar kwamitin za ta isa yankin da zarar aka shawo kan tsiyayyar man.

A cikin ‘Yan kwanakin nan an samu yawaitar satar gurbataccen mai a yankin da kamfanin na Shell ke gudanar da ayyukansa, lamarin da kuma ya tilastawa kamfanin rufe wasu daga cikin rijiyoyinsa saboda dalilai na tsaro.

Kamfanin ya ce a irin wannan yanayi, da wuya ya iya samar wa kasuwar duniya adadin gangunan mai maras nauyi da ya kamata ya samar a kowace rana.

Alkalumma dai sun yi nuni da cewa akalla dalar Amurka Milyan dubu shida ne Najeriya ke hasara a kowace shekara sakamakon satar gurbataccen mai, yayin da ake danganta wannan matsala da matasan yankin da suka mayar da fasa bututu domin sata a matsayin wata babbar sana’a da ke samar da makuddan kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.