Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta dakatar da gudanar da zaben ‘Yan Majalisu

Kotun kasar Masar ta dakatar da gudanar da zaben ‘Yan majalisar dokokin da aka shirya yi a ranar 22 ga watan Afrilu, al’amarin da ya sake jefa gwamnatin Mohamed Morsi cikin rudani. Kotun tace akwai bukatar sake bitar dokokin zabe a kotun kolin kasar.

Shugaban Masar Mohamed Morsi a zauren taron shugabannin kasashen Musulmi
Shugaban Masar Mohamed Morsi a zauren taron shugabannin kasashen Musulmi REUTERS/Egyptian Presidency/Handout
Talla

A cikin wani dan takaitacen jawabi da ya yi, shugaba Morsi ya bayyana cewa, yana mutunta tsarin shara’a da kundin tsarin mulki da ka’idodin kasa da kuma rabe raben mulki, sai dai kuma bai fito fili ya nuna ko zai daukaka kara ba.

A watan jiya ne shugaba Morsi ya bayar da sanarwar gudanar da zaben ‘Yan Majalisu a ranar 22 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.