Isa ga babban shafi
Masar

An saka ranar sake yiwa Hosni Mubarak sabuwar shari’a

Hukumomin Kasar Masar sun ce za’a sake yiwa Tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak shari’a daga ranar 13 ga watan gobe, saboda zargin da ake masa na hannu wajen kashe masu zanga zanga.

Talla

Wata kotun daukaka kara ta soke daurin rai da ran da aka masa, ta kuma bada umurnin sake shari’ar ta sa, tare da wasu jami’ansa, da suka hada da tsohon ministan cikin gida, Habib al-Adly da wasu manyan jami’an tsaro shida.

An dai yankewa Mubarak da Adly hukuncin kisa ne a ranar 2 ga watan Yunin bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.