Isa ga babban shafi
Masar

An jibge ‘Yan sandan kwantar da tarzoma kusa da fadar Shugaban kasar Masar

An jibge ‘Yan sandan kwantar da tarzoma domin tsare fadar shugaban kasar Masar, Muhammed Morsi, wanda ‘Yan adawa su yi ta kaiwa hari a jiya Juma’a a dai dai lokacin da hukumomin kasar ke kokarin kwantar da wata sabuwar tarzoma da biyo bayan wani hotan Bidiyo da ya nuna wasu ‘Yan sanda na jibgan wani mutum dake tsirara.

Lokacin da masu zanga zanga ke arangama da 'Yan sanda a Masar
Lokacin da masu zanga zanga ke arangama da 'Yan sanda a Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

A can Dandalin Tahrir Sqaure kuwa, rahotannin sun nuna cewa daruruwan masu zanga zanga sun kai hari kan jerin gwanon motocin Firaministan kasar, Hisahm Qandil, inda suka yi ta hurga duwatsu a lokacain da ya kai ziyara yankin bayan wata fito na fito da aka yi tsakanin ‘Yan sanda da ‘Yan adawa a daren jiya Juma’a.

Arangamar ta jiya, ta yi sanadiyar mutuwar wani dan shekaru 23 wanda aka zargi ‘Yan sanda da harbe shi a yayin da suke harba yaji mai sa hawaye don kwantar da tazomar.

Tuni dai fadar shugaban kasar ta nuna alhininta game da wannan hotan Bidiyo da ke nuna ‘Yan sanda na dukan mutumin, a wata rubutacciyar sanarwa da ta fitar, inda ta ce ya sabawa mutunta Dan adam.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.