Isa ga babban shafi
malawi

An cafke mutane 11 da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Malawi

‘Yan Sanda a kasar Malawi sun cafke mutane 11 da suke zargi sun yi yunkurin juyin mulki, wadanda suka hada har da kanin marigayi tsohon shugaban kasa, Bingu Wa Mutharika da Ministocin tsohuwar gwamnatin shi.

Shugaban kasar Malawi Joyce Banda
Shugaban kasar Malawi Joyce Banda Reuters
Talla

Ana zargin mutanen ne da yunkurin hana Joyce Banda, shugaban kasar mai ci, hawa karagar mulki bayan mutuwar Mutharika a bara.

Cikin wadanda aka cafke sun hada da Tsohon Ministan harakokin wajen kasar Peter Mutharika wanda kani ne ga shugaba Mutharika.

Ana dai hasashen mutanen za su iya fuskantar hukuncin kisa idan har aka gano sun ci amanar kasa.

Wata majiya daga ‘Yan sandan kasar tace cikin wadanda aka cafke sun hada da tsohon Ministan kananan hukumomi da Ministan watsa labarai da Ministan kudi da kuma na wasanni tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Bayan cafke mutanen, ‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a harabar hedikwatar ‘Yan Sanda.

A ranar Bakwai ga watan Afrilu ne aka rantsar da Banda a matsayin sabuwar shugabar kasar Malawi bayan mutuwar Mutharika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.