Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan da Sudan ta Kudu sun janye dakaraunsa daga kan iyaka

Dakarun kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun janye daga kan iyakar da kasashen biyu ke takaddama a kai, wanda hakan zai ba da damar barin kan iyakar ba tare da tsaron sojoji ba.

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir (hagu) da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir (dama)
Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir (hagu) da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir (dama)
Talla

“Duka kasashen sun cika bukatun da ake nema daga garesu, wanda ya shafi janye dakaru daga kan iyaka.” Inji Kungiyar Nahiyar Afrika ta AU bayan Ministocin Tsaron kasashen biyu sun gana a kasar Habasha.

Wannan dai na nufin za a samu damar magance matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a kan iyakokin kasashen biyu, sai dai masu sharhi akan rikicin na kasashen, sun ce zai yi wuya a samu mafita game da tsaron kan iyakokin kasashen.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.