Isa ga babban shafi
Masar

Mutane da dama sun jikkata a sabon rikicin Addini a Masar

Sama da mutane 80 suka jikkata tare da samun mutuwar mutum guda a rikicin da ya barke tsakanin Musulmi da Kirista a lokacin da ake bukin jana’izar wasu Kiristoci hudu da aka kashe a makon jiya.

'Yan sanda suna arangama da masu zanga-zanga a kasar Masar
'Yan sanda suna arangama da masu zanga-zanga a kasar Masar Reuters
Talla

Sabon rikicin da ke kunno kai tsakanin Musulmi da Kirista na dada cusa shakku ga kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar Masar bayan mabiya addinan biyu sun hada kai waje daya domin hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak a shekarar 2011.

Kamfanin Dillacin labaran Masar na MENA ya ruwaito cewa akalla mutane 84 suka jikkata bayan kwashe sa’o’I ana bata kashi tsakanin Musulmi da Kirista inda suka yi musayar duwastu da harba karamin bom da aka samar da Fetir.

An samu mutuwar wani mutum Kirista mai suna Mahrous Hana Tadros, mai shekaru 30.

‘Yan sanda kasar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa gungun masu rikicin. An ruwaito ‘Yan sanda 11 ne suka samu rauni.

Daga cikin wadanda ke rikicin sun ta amfani da kalaman batanci ga shugaba Morsi na Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi suna masu kiran lalle sai shugaban ya yi murabus.

Sai da kuma Shugaba Morsi ya yi Allah waddai da rikicin yana mai shedawa babban jagoran mabiya Kirista Fafaroma Tawadros na II cewar duk wani hari da aka kai wa Kirista kamar shi ne aka kai wa harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.