Kotu ta jingine zargin yunkurin kashe shugaban Benin da ake yi wasu mutane
Alkalin wata kotu a birnin Cotonou da ke Jamhuriyar Benin, ya yi watsi da karar da bangaren gwamnatin kasar ya shigar a gabansa bisa zargin wani shahrarren dan kasuwa na kasar mai suna Patrice Talon kan cewa ya yi kokarin kashe shugaban kasar Bony Yayi ta hanyar sanya masa guba.
Wallafawa ranar:
A cikin watan oktoban da ya gabata ne dai mai shigar da kara na gwamnatin kasar, ya bayar da umurnin cafke Patrice Talon wanda a lokacin ya ke zaune a Faransa, da likitan shugaban kasar da kuma wata ‘yar uwarsa, bisa zargin cewa sun hada baki domin kashe shugaba Bony Yayi.
A ranar 22 ga wannan wata ne dai ya kamata wata kotu a birnin Paris ta yanke hukunci a game da yiwuwar tuso keyar Patrice Talon zuwa kasarsa domin ya fuskanci wannan zargi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu