Isa ga babban shafi
Najeria

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudurin dokar haramta auren jinsi daya

Majalisar dokoki a Tarayyar Najeriya, ta jefa kuri’ar amincewa da wata sabuwar doka da ta tanadi hukuncin dauri na tsawon shekaru 14 ga wadanda aka samu da yin auren jinsi guda.

Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Aminu Tambuwal
Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Aminu Tambuwal nigeriansabroadlive.com
Talla

Haka kuma dokar ta tanadi hukuncin daurin shekaru 10 ga jinsi daya mata ko kuma maza da aka samu da laifin bayyana soyayya ga juna a zahiri ko aka samu mutum da laifin halartar wani taro da ya shafi hakan.

Mambobin Majalisar Wakilan kasar ne dai suka amince da wannan doka da gagarumin rinjaye, wadda tuni majalisar dattawan kasar ta amince da ita.

A watannin baya dai, Firaministan Birtaniya, David Cameron, ya yi barazanar cewa kasarsa za ta rage irin tallafin da take bai wa kasashen da suka ki amincewa da auren jinsi daya.

Hakan kuma ya sa wasu da dama na ganin dokar na iya kawo cikasa ga irin tallafin da ake bawa kasar domin yaki da cutar AIDS ko kuma SIDA. Ita ma kasar Amurka ta nuna damuwarta akan wannan doka tun da farko, inda Shugaba Barack Obama ya umurci dukkanin ofisoshin jakadancin kasar su dauki matakan jaddada bukatar bawa masu auren na jinsi daya damar yin abin da su ke so.

Batun auren jinsi daya a Najeriya, batu ne da ya kasance haramtacce tun bayan samun mulkin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekarar 1960.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.