Isa ga babban shafi
Najeriya-Lebanon

An gano wani gida shake da makaman Hezbollah a Kano

Jami’an tsaron Najeriya sun yi ikirarin gano wani gida a garin Kano shakare da makamai da suka ce na Mayakan Kungiyar Hezbollah ta Lebenon da suka aje don kai wa Turawa da Yahudawan Isra’ila hari a Najeriya.

Wasu Makaman kungiyar Hezbollah ta Iran
Wasu Makaman kungiyar Hezbollah ta Iran REUTERS/Amir Cohen
Talla

Rundunar sojin Najeriya tare da Jami’an tsaro na farin kaya sun alakanta gidan da ke unguwar Bompai a matsayin mabuyar ‘Yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Makaman da aka samu sun hada da rokoki da manyan bindigogi masu sarrafa kansu da sauransu.

Akwai wasu ‘yan kasar Lebenon da aka cafke da ake zargi suna da alaka da ajiye makaman

Babban Daraktan Jami’an tsaron farin kaya Bassey Etang ya tabbatar wa manema labarai  cewar an ajiye makaman ne domin kai ‘Yan kasar Isra’ila hari da kuma Turawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.