Isa ga babban shafi
Lebanon

Hezbollah Zata kafa Gwamnatin dukkanin Jam'iyyu idan ta samu Nasara

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, ta yi alkawarin sanya 'yan adawa cikin gwamnati, mudin a ka zabi wanta tsayar a matsayin sabon Prime Ministan kasar.Shugaban kungiyar Hassan Nasrallah ya ce, idan dan adawa ya samu nasara, zasu bukace shi ya kafa gwamnati, amma idan su suka samu nasara, to su zasu kafa gwamnati, tare da sauran jam’iyyu.Idan dai ba a manta ba, gwamnatin Prime Minista Saad Hariri, ta fadi sakamakon janyewar ministocin kungiyar Hezbollah da masu kawance dasu. Binciken kisan da a ka yi wa tsohon Prime Minsitan kasar Rafik Hariri, ya janyo rushewar gwamnati, saboda rade radin cewa ana zargin kungiyar ta Hezbollah da hanu a ciki.

Reuters/Ali Hashisho
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.