Isa ga babban shafi

Mali: Ƴara dubu 80 na ƙarkashin ƙawanyar ƴan ta'adda a Meneka -Save the Children

Ƙungiyar agaji da ke bai wa yara kariya ‘Save the Children’ ta ce ƙawanyar da mayaƙa masu ikirarin jihadi suka yi wa garin Menaka a Mali, ya rutsa da mutane kimanin dubu 140, cikinsu har da ƙanan yara akalla dubu 80.

Kungiyar agaji da ke bai wa yara kariya ‘Save the Children’ ta ce ƙawanyar da mayaƙan ‘yan ta’adda suka yi wa garin Menaka a Mali, ya rutsa da mutane kimanin dubu 140, cikinsu har da ƙanan yara akalla dubu 80.
Kungiyar agaji da ke bai wa yara kariya ‘Save the Children’ ta ce ƙawanyar da mayaƙan ‘yan ta’adda suka yi wa garin Menaka a Mali, ya rutsa da mutane kimanin dubu 140, cikinsu har da ƙanan yara akalla dubu 80. AFP/File
Talla

Tuni dai ƙofar ragon da ‘yan ta’addan suka yi wa garin na Menaka ya jefa dubbban ƙanan yaran cikin tashin hankali, inda suke fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki, da kuma ɓarkewar cututtuka.

Ƙawanyar da ‘yan ta’adda suka shafe watanni huɗu suna yi wa Menaka dai iri guda ne da ƙanshin mutuwar da mayakan suka fara yi wa birnin Timbuktu tun daga watan Agustan shekarar bara, wanda kuma har yanzu basu janye ba, ko da yake lokaci zuwa lokaci akan shigar da kayayyakin agaji zuwa birnin.

Bukatar jinkai

A halin yanzu dai karancin muhimman kayayyakin masarufi da magunguna yayi tsanani ga al’ummar Menaka, birnin da ke karɓar baƙuncin ‘yan gudun hijira akalla dubu 33 da 600, waɗanda suka tserewa hare-haren ta’addanci a wasu sassan kasar Mali.

Jami’ar kungiyar agajin ƙasa da ƙasan ta ‘Save the Children’ sun tattara waɗannan bayanai ne, bayan da suka samu damar shiga birnin na Menaka da zummar gudanar da bincke kan halin da jama’a ke ciki, amma kuma suka maƙale har tsawon makwanni uku, kafin su tsallake rijiya da baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.