Isa ga babban shafi
Afrika

Kofi Annan ya ce Afirka ce ta fi cutuwa da matsalar kin biyan haraji

Tsohon magatakarda na Majalisar Doinkin Duniya Kofi Annan, ya bayyana takaicinsa a game da yadda kasashen Afirka ke asarar bilyoyin kudade a kowace shekara, sakamakon yadda kamfanoni da kuma attajirai ke kin biyan haraji a nahiyar.

Kofi Annan, na gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Kofi Annan, na gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Kofi Annan, wanda ke gabatar da jawabi ga mahalarta taron da Kwamitin Tsaro na MDD ke gudanarwa domin rigakahin faruwar rikice-rikice, ya bayar da misali da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, inda ya ce kasar ta yi asarar dala bilyan daya da milyan 400 daga shekara ta 2010 zuwa 2012.

Annan, ya ce Afirka ce ta fi fuskantar wannan matsala, inda kamfanonin hako ma’adinai ke amfani da hanyoyi na rashawa domin kin biyan harajin da ya kamata su biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.